Close

AMON ‘YANCI

By Halima Ahmad Matazu

English translation of this story is published here.

Litinin
5 ga Yuni 2000

Kalaman karshe da za ta iya tanatancewa daga bakin alkali su ne,”hukuncin kisa, ta hanyar ratayewa.” Bayan su kuwa ba ta sake fahimtar komai ba. Sannu a hankali ta dago da kan ta, ta dubi fuskar Pamela, wadda ke cike da kidima da alamar tambaya. Ta runtse idanuwanta, don ta yi kokarin tsai da hawayen da ke neman su butulce mata, ta kuma bude su. Nan take, ta soma ganin abubuwa na yi mata gizo. Amon bugun zuciyarta, tamkar a cikin kunnuwanta dama can a ka halitta shi, kafafuwanta kuwa, sam ba ta jin su a tattare da ita. Daga nan, kada ku kuma tambaryata me ya sake wanzuwa a dakin kotun, ita kanta ba za ta iya tuna komai ba.

Nan take ta soma ganin wani irin haske, tamkar a cikin gajimare. A cikin yanayin kuwa ta riski kanta tamkar tana ‘yar kimanin shekara goma. Kakarta Nana kuma tana a raye. Ta dora kanta a kan cinyoyinta. Kalamanta masu sanyaya zuciyar da ke cikin rudani, muryarta tattausa, amon ta tamkar busar sarewa, ta ambaci sunanta, ” Maryama, imani da kaddara wani muhimmin al’amari ne da zai iya kwantar maki da hankali a duk lokacin da wata musiba ta auku. Musamman idan kika yi la’akari da cewa, ubangijinki mai rangwame ne ga bayinsa. Don haka, matukar kika yi tawakkali da hukuncinsa, to za ki samu sakamako a ran gobe kiyama, sakamako babba da har ba ya iya misaltuwa.

Ki yi nazari Maryama, tare da aiki da shi, wanda hakan shi zai maye gurbin duk wata damuwa ya zuwa farin cikinki,har ma hakan ya shafi wanda yake tare da ke.’’
Ta tada kai, ta dubi cikin kwayar idanuwan Nana,wadanda ke cike da annuri, tamkar suna yin albishir mai faranta rayuwar da ke cike da rashin sanin madafa. Murmushinta a sanyaye, ta kuma duban fuskarta, ta lumshe idanuwana, tare da kara kanannade jikinta, don ta rabi dumin jikinta.

Hawaye zazzafa suka kwaranya a fuskarta. Kalaman Nana a kodayaushe sukan kara mata karfin gwiwar da har ta kan manta, da halin kunci da ta riski kanta a ciki. Ta saki dan murmushi tare da duban kwayar idanuwan Nana, wadanda a lokacin, suke rikidewa suna komawa na Pamela. Ta mika hannayenta don ta riko hannayen Nana, amma tamkar Nana na dushewa a cikin hazo. Sannu a hankali ta bude idanuwanta gaba daya, wadanda suka ci karo da fuskar Pamela.

Ta dan dudduba muhallin da ta ke,wanda ba ko tantama tana kwance ne a kan gadon asibiti, ta kuma duban Pamela da ke zaune a gefen gadon. Can dayan gefen kuma, wani mutum ne daban ke tsaye da wata mata, suna magana da harshen turanci.Wanda ga dukkan alama dai ma’aikatan jinya ne su biyun. Ga yanayin shigarsu za ka iya fahimtar hakan. Daga bakin kofar dakin kuwa, idanuwanta kan riski wani dan sanda dauke da bindiga, ga dukkan alama a dalilinta ya ke zaman aikin gadin. Pamela ta dan saki murmushi ta ce,”Ya jikin ki?” Mairo ta gyada mata kai, ta kuma ce mata,”Me ya kawo mu nan kuma?” Pamela ta yi ajiyar zuciya ta ce,”Har kin manta da abin da ya wakana ne…?” Take yanke al’amurran da suka wakana a dakin kotun suka dinga bijirowa a cikin kanta daya bayan daya. Ta dan dafa goshinta, bayan da ta ji wani zugi na ciwo. A wurin kuma, bandeji ne da aka daure raunin da ta ji, bayan da ta fadi a sume cikin dakin kotun. Mairo ta yi ta kokarin tuna kalaman alkalin wadanda a zahiri ba su ba ta mamaki ba, ganin yadda wancan lauyan nata na farko, ya rika nuna halin ko in kula, don ya kare ta daga laifin kisan kan da a ka tuhume ta a kansa. Amma kuma wani abin mamaki, sai kuma ga shi yanzu hankalinta a kwance, kamar tsumma a randa, kwata-kwata ba ta fargabar komai, don a lokacin babu wani abu daya na rayuwar duniya da ke da muhimmanci a cikin rayuwarta.

Bayan da ma’aikacin jinyar, wanda ta fahimci cewa likita ne ya salami ma’aikaciyar jinyar ya karaso inda take kwance, ya dudduba halin da take ciki, tare da yi mata bayanan da a zahirin gaskiya bata fahimci komai daga ciki ba. Fitarsa dakin ke da wuya, ta yi yunkurin tashi daga zaune, to amma ga alama hakan ba za ta samu cikin jin dadi ba. Hakan ya sa Pamela ta taimaka mata ta tashi. Ta dubi tagar da ke dakin, ga alama dai almuru ya sauka,ko don a zahiri bata damu da ta san ko karfe nawa ne ba. Pamela da ke ta kokarin zuba mata ruwan shayi, ta dube ta a kaikaice ta ce,”Hala ma dai yau Nana ta kawo mana ziyara ne, na ji kin ambaci sunanta a cikin barcin ki? ” Mairo bata kula da ta ba ta amsa ba, ta da karbi kofin shayin tare da yi mata godiya. ”Hattara dai!” Pamela ta ambata. Mairo ta dubeta, kana ta dubi doron cikinta wanda ga alama shi take zance a kai. Kunya ta kamata, don sai a lokacin ta ankara da irin motsin da dan tayin da take dauke da shi yake yi mata a ciki. Ya Allah ko don matsananciyar yunwar da take ji ce, oho? Bayan ta hadidiye magungunan da Pamela ta miko mata, wato irin wadanda mata ma su juna biyu ke hadiya kullum don kare lafiyarsu, da ta abin da suke dauke da shi ne, idanuwanta suka riski wata jarida a kan teburin da ke gefen gado, wadda a jikin shafinta na farko hoto Mairo ne, kamar dai kusan kodayaushe. Pamela ta janyo kujera ta matso dab da inda take a kishingide ta janyo jaridar ta miko mata.” Abishirinki, mun daga kara zuwa babbar kotun majistare . Kuma nan da sati uku za a fara sauraren karar. Kin ma san wani abin farin ciki ? wata kungiyar kare hakkin dan adam mai zaman kanta da ke Amurka ta yi Allah wadai da wannan hukunci da a ka zartar,haka kuma kungiyoyin mata da na matasa daban-daban duk sun yi Allah wadai da wannan hukuncin, don wadansun su ma sun kudirci yin zanga-zangar lumana a kan wannan hukuncin da kotu ta zartar…” Pamela ta dan yi shiru kana ta sa hannu ta girgiza kafadar Mairo, bayan da ta lura cewa ba ma saurarenta ta ke ba, don hasali ma hankalinta ba ya kan zancen da take ta zubawa kamar kanyar da ba dadi. Mairo ta saki dogon tsoron kitsonta da take wasa da shi, ta dubi Pamela ta wutsiyar ido ta ce, ”Ina sauraren ki mana, ba kina zancen dage kara ba ne?”
Pamela ta dan bata fuska ta ce ” Mairo na lura kamar ba ki da sha’awar zancen da na ke,…wato kamar ba ya da muhimmanci a wajen ki, hasali ma dai ba ki dauki ‘yancin rayuwarki da muhimmanci ba. Mairo idan na fahimce ki na dan tsawon lokacin nan da nake ta fafutukar neman ‘yancinki, zan iya cewa kin sadaukar da wata aba wai ita rayuwa gabakidaya.Sau tari na sha bayyana maki cewa idan kika yi hakan, to ba ki yi ma kanki adalci ba ,ni din nan ba ki yi mani adalci ba, haka sauran jama’ar da ke goyon bayanmu, ba ki yi masu adalci ba. Rashin ba da hadin kanki, dan haka ta cim ma ruwa, yana kawo tangarda matuka ga yanayin aikina. Mairo,… ba wai fa na ce lallai sai kin yi imani da abin da nake ta fafutuka a kai ba, idan har kina ganin aikin da nake shirme ne,to akalla ba za ki so a ce dan da kike dauke da shi ya tashi cikin walwala da ‘yancin rayuwa ba, ko kin kwammace a ce tarihi ya maimaita kansa? Shin Mairo kina tunanin cewa idan har Allah ya raya abin da ki ke dauke da shi, zai taba yafe maki muddin ya san gaskiyar al’amarin cewa ke da kanki kika zaba ma kanki rashin ‘yanci da ya haddasa masa rayuwar maraici. Mairo na yi imani da cewa dan da za ki haifa zai yi alfahari da ke a matsayinki na uwa, kuma jaruma wadda aka rattaba a cikin kundin tarihi,wadda ba ta yarda ‘yancin ta ya tafi a iska ba, ba tare da ta yi fafutukar kwato ma kanta hakkinta na rayuwa ba. Mairo, koda kina kwance a turabi, ba kya fatan a ce kin bar ma na baya da tarihi, kin zamo abar kwatance da za ki iya sauya tunanin mutane da dama, da suka tsinci kawunansu a matsayi irin wannan? Ni a nawa ra’ayin, ina ganin idan har kika sake ‘yancinki ya tafi a iska, to ba ki yi ma rayuwar ki adalci ba, kuma kin zalunci kanki da masoyanki, kuma Allah ma ba zai bar ki haka nan ba.”

Duk wanan zancen da Pamela ke yi Mairo na dai saurarenta ne kawai, amma takaici tattare da tausayinta ya kama ta. Alal hakika a iya rayuwarta bata taba ganin mace mai nacin tsiya da yawan surutu irin Pamela ba, hasali ma tana ganin, aikinta na lauya ya dace da yanayinta.

Ita dai Pamela lauya ce mai zaman kanta, tana aiki tare da wata kungiya ta kare hakkin mata da yara mai zaman kanta da ke da hedikwatarta a Balma. Pamela ta tsinci shari’ar da rana tsaka, kuma ta ga ya dace a ce kungiyar ta su, ta saka baki a kan shariar don sun lura cewa babu adalci a cikin ta. Pamela mace ce mai tsananin akida, ba ta san wani abu wai shi rashin cin nasara ba,sai dai a ra’ayin Mairo, tana ganin wannan karon dole ta sauya yanayin tunaninta, duk da ta san Pamela ta sadaukar da lokuttanta don ganin sun ci nasara a kotu.
Alal hakika Pamela ta yi iya kokarinta na jero hujjojin da suka nisantar da Mairo daga tuhumar da ake yi mata a kotu, to amma sai ga shi alkalin ya sa kafa yayi fatali da duk wata hujja da Pamela ta zayyana, har ya yanke ma Mairo hukuncin kisa.

Cikin bacin rai Mairo ta dago da kanta, ta dubi Pamela cikin idanuwan nan nata, masu launin rowan zuma ta ce, ” ‘Yanci! ‘yanci!! Wai ke ba ki da wani zancen da ya wuce wannan? Wai jira ma na tambaye ki, Pamela kin ga alamar ina da bukatar taimakon da ki ke ta fafutukar nema a kaina, ba kya ganin kun so ku makara?” Pamela ta yatsana fuska, ta ce ” Kamar ya mun so mu makara, ban fahimce ki ba?” Na saki kan murmushi tare da ajiyar zucciya, na ce ”lallai kuwa ba za ki iya ki fahimta ba,don bakin alkalami ya riga ya bushe. Pamela, na tabbata akwai wadanda suka fi bukatar taimako irin wanda kike kokarin yi a kaina bila adadin. Abin da ya fi daure mani kai shi ne, don me ki ke bata lokacinki a kai na? Sa’adda na tozarta da kalamai masu matukar kuna, da salwanta tunanin dan adam, ya zamo baya da akalar da zai jagoranci rayuwa mai yalwa, kina a ina? Pamela, na rasa rayuwata ta kuruciya tun ba na iya tantance tsakanin dama da hagu, aka dora ni bisa turbar shiga rayuwar da linzaminta, ya fi karfin ragamar da aka danka a gare ni. Ya ba ki zo kika fanshe ni ba ?

Shin ko kin san na kwana a karkashin taurari, na rufa da mayafin babu a tsakiyar hunturu wai da nufin jaura ta bi ta kaina, ko don na huta da rayuwa bakidaya?

Pamela, na kwana na yini ban ci ba, hasali ma na yi karin kumallo kwano daya da Karen gidanmu. Duba ki ga ni Pamela.” Na kware mata gadon bayana, wanda ya sha ado da sawun dorina. “Sa’adda fata ta ke fitar da amon jini, kina ina? Shin ko kin san na kasance tamkar ‘yar tsana a gurin Baffa ummaru a cikin duhun zauren gidan mahaifina, a lokacin na koka amma ba ki zo kika agaza mani ba. Na yi rashin ginshikaina a rayuwa, na zamo ba ni da madafa, na zamo tamkar baiwa da abar kyamata a gidan miji. Duka a gun mijina tamkar Karin kumallon sa ne a jikina.wa ya zo ya agaza ma ni? Pamela ina kike, ina ire irenkun masu ikirarin kare hakkin dan adam? Me ya yi saura a nan?!” Mairo ta nuna jikinta. “Oho! Ashe fa duk kin karanta a cikin littafin adana bayanan sirri na. Duk wani ‘yanci da kike ganin ina bukata a yanzu, bai yi ya ‘yancin da na rasa ba tun a baya, wanda ba ma ke ba, duk fadin duniyar nan ban ga mai iya maido mani da shi ba!”

Mairo ta fada ta juya tana kallon taga, ba ta son Pamela ta ga hawayen da ke zuba a fuskarta, can ta share fuskarta da bayan hannunta, ta yi murmushin karfin hali. ”Wannan dan tayin da nake dauke da shi, ba kansa farau maraici ba. Ai ba a maraya sai raggo. Na tabbata da akwai bayin Allah salihai da ba sa karewa, kuma ba za a rasa wanda zai rene shi ba har Allah ya raya shi, ya zamo abin alfahari a cikin al’ummar annabi. Ki sani da ni da babu ni abin da duk Allah ya hukunta a kansa, babu ko shakka sai ya tabbata. Pamela duk wani taimako da kike ganin za ki iya yi a gare ni, ba zai yi wani tasiri ba. Na yi imani har ga Allah ke mace ce tagari. Ka da ki tsaya bata lokacinki, a kaina, kin riga kin sani ba ki da wata madafa kwakkwara da za ta yi ma ki tasiri a kotu”. Mairo ta fada tamkar tana yi mata magiya. Pamela ta gyada kanta, tare da dan gajeran murmushi da ya bayyana kyawawan hakoranta, ya sakaya damuwar da ke shinfide a fuskarta a sanyaye ta ce, ”Gaskiya ne, bani da wata madafa kwakkwara, da za ta iya yi mana tasiri wajen ganin mun ci nasara a gaban kuliya. Dalili kuwa, matsalar na a wajen ki Mairo! Saboda ina iya bakin kokarina,don na sami duk wadan su bayanai kwarara a wajenki, amma kin ki, ki ba da hadin kai yadda ya kamata.

Ba shakka, sun shiga gabanmu ta yadda duk ba kya tsammani, dalili kuwa, akasarin jama’a yanzu idanuwansu sun rufe da kwadayin abin duniya. Kwata-kwata idanuwansu sun dushe ba sa ganin abin da ke cikin zukatansu, hankullansu sun fi raja’a akan kwadayin abinda bai taka kara ya karya ba. Kuma abin takaici, a cikin manyanmu, da su ke da alhakin dai-daita sahun al’ummominsu, kuma su al’umma suka ta’allaka komai nasu na rayuwarsu a garesu, a ke samun bata gari, wadanda su ne a sahun gaba wajen gurbata tunanin al’umominsu, da sauya alkiblar rayuwarsu, ta zamo cikin kunci da halin kaka ni ka yi. Amma ina son ki lura da wani abu daya Mairo, kina zaton da akwai wani mahalukin da ya isa ya sakaya gaskiya bayan Allah ya bayyanar da ita a fili? Ko da kike ganin kamar sun yi nasara a kanmu, har yanzu da sauran rina a kaba.

Mairo…, na tabbatar da cewa rayuwa ba ta yi maki adalci ba, kin hadu da musibu iri-iri wadanda bai kamata a ce a iya ‘yan shekarunki, ya dace a ce sun yi tasiri a kanki ba.Sai dai da za ki lura, da akwai yara da dama, wadanda ke kin fi su cin ribar rayuwa, domin dai ke Allah ya baki dammar da kin yi ilimi dai-dai gwargwado da za ki iya alfahari da shi. Ko kin lura da yaran da ke a kan manyan hanyoyi da aka dora masu tere tankame da biredi, ko fiya wata, ko kuma waccan yarinyar da ke kan layi tana jiran kwastama, su fa wadan can da ke a karkashin gadoji suna zukar hayakin barasa ana amfani da su wajen bangar siyasa? Mairo, ki tuna da kasahen da ke fama da masifar yake-yake,da yaran da a kalla ba a kasaru ba su 200,000 a nahiyar nan ta mu, ta Afrika da aka mallaka ma su bindigogi a maimakon alkalluma suna jin duniyar kamar a tafin hannayensu take. Mairo wadannan mafi yawancinsu yara ne da aka kangarar da tunaninsu, kwata-kwata rayukansu ba su san da wani abu wai shi ‘yanci ba, ballantana su ci gajiyar kurucciyarsu. Na sani cewa ban agaza maki ba, a lokacin da kika fi bukatar a agaza maki matuka, watakila da ba ki tsinci kanki a cikin wannan yanayin ba. Kuma koda na san cewa muna da banbancin addini, amma na san na karu da abubuwa da dama daga wajen Maigidana da suka shafi addinin Islama. Mairo na san cewa Ubangiji yana shinfida ma kowane bawa kaddararsa ,kuma Yana jarabtar bawansa ta hanyar sa shi cikin musiba iri-iri, don ya gwada imanin sa, don ya zama darasi ga mutane.

Mairo ki tuna fa, ko a cikin littafinku mai tsarki ubangiji ya ambaci cewa duk halin da bawansa ya sami kansa, kuma ya yi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau, idan ya yi tawakkali da cewa ko mai yana da dalili da kayyadadden lokaci, to zai ga sakamako babba abin mutuntawa.

Na sani ba wanda zai iya maido maki da ‘yancinki da kika rasa a rayuwarki. Amma kin san da za ki yi kokarin yafe ma kanki, kafin ma duk wani da ki ke ganin ya jaza maki matsala a rayuwarki, da kin cike gurbin da kike ganin kin rasa a baya. Dalili kuwa, jiya ta riga ta wuce, duk wani bacin rai, ko danasani ba zai taba maido maki da rayuwar baya ba, illa ki yi kokarin gyara yanzu, ba ma gobe ba tukuna, tunda goben sai mai rabon gani.”

Pamela ta dan dubi agogon hanunta, bayan da ta ji sautin muryar ladani na gayyatar jama’a zuwa ga sallar magariba, ta ja dan numfashi ta kuma cewa, ”Mairo, wata kila ke din nan wata aya ce ga al’umma, da za ki iya sauya tunanin mutane da su hankalta. Duk wanda ya rayu, rayuwa irin taki kuma har ya kawo wani lokaci da ubangiji ya nuna shi ga duniya, tabbas akwai wata martaba a tattare da al’amarinsa. Mairo ko kina ganin Allah zai bar ki, ki wulakanta, kuma ki tashi a tutar babu?” Pamela ta matso kusa da ita, ta sa hannunta, ta dago da fuskarta, wadda a lokacin hawaye zazzafa ke kwaranya a kanta, cikin tattausar murya mai kama da ta Nana, ta kuma cewa. ” Mairo, na yi imani da cewa ke din nan, kina da wata baiwa a tattare da ke, wadda tun sa’ad da nake aikin lauya, yau shekara ashirin da daya, ban taba haduwa da shari’a irin taki ba, da na rasa sukuni,al’amarinki na da ban mamaki,ban taba haduwa da mutumin da kwata-kwata zuciyarsa ta kekashe ba ya da ra’ayin dora wata rayuwa a gabansa ba, sai ke Mairo” Pamela ta ja ‘yar gajeruwar ajiyar zuciya , ta nade hannayenta a kirjinta, ta kura ma Mairo idanuwa.

Mairo ta girgiza kanta, duk da kuwa ta tabbata da cewa da akwai barbashin gaskiya ga kalaman Pamela ta ce, ”Ba za ki iya fahimta ba ne Pamela.” Cikin mamaki ta daga girar ido daya ta ce,” Ka da fa ki manta, kin san na iya sauraren mutane da kyau da kyau ko, me zai hana ki fahimtar da ni ko na gane?” Mairo takuma dubanta ta ce, ” Wai ke don Allah ba kya gajiya da surutu ne?” Pamela ta dan yi murmushi ta ce, ”kin manta shi a ka koyar da ni, kuma da shi nake alfahari? Mairo ta saki ‘yar gajeruwar dariya ta ce, ” Amma kuwa an koyar da ke shirme, wai ta ya za a iya a koya ma mutum yawan surutu ne har ya yi alfahari da hakan?” Pamela ta dan kanne ido daya ta sunkuyo kusa da ita ta ce, ” Kina son ki sani ne?” Mairo ta dan yi jim, ta ce. ” Eeh, to zan so na sa ni.” Ta ce, ”To shi kenan,amma fa abin sirri ne, idan kin yarda a yi ta Bahaushe, ba ni gishiri in ba ki manda.” Mairo ta zumbure baki ta ce, “kamar ya?” Pamela ta gyara zama ta ce, ” Idan kin yarda, ina nufin ki bani cikakken hadin kai, da duk bayanan da nake nema, ni kuma na sha alwashin daukar nauyin karatunki, har sai kin koyo yawan surutu kamar ni” Mairo ta kuma tabe baki na ce, “Amma fa Pamela ina jin har da wayo ake koya maku ko?” Suka tintsire da dariya bakikaya, Pamela ta ce ” Haba ko ke fa, kin ga yadda dariya ke yi maki kyau?”

Kaico! Wadannan kalamai na Pamela sun hankako ma Mairo da ire-iren kalaman da Bawuro ke yi mata, shekaru da dama da suka gabata. Rabon da ta yi dariya makamanciyar wannan ita kanta ba ta iya tunawa.

***********************************************************************

Mairo ta juya bangaren hagu a kan dan gadonta ta kura wa ‘yar taga kwaya daya tal da ke a dan dakin fursunanta ido.Hasken farin wata ya rarratso karafan da ke a jikin tagar, bayan da wani girgijin ya yaye haskensa gabadaya. In banda kukan wata mujiya da ke a bisa reshen wata bishiyar gawo, da idanuwanta kan riska, ba ta jin motsin komai, hatta sautin tafiyar gandurobar da ta kan ji a kai a kai sam ya dauke. Ta dubi watan da ke ta rarratsa giza-gizai, tausayinsa ya kama ta,don shi ma kamar ita a irin nata tunanin yana tattare da kewa, don ko ga alama bata hango zahra a kusa da shi ba.Sai dai ga alama shi ya fi ta ‘yanci da walwala. A dai-dai lokacin ta ji dan tayin da ke cikinta ya kai mati harbi, hakan ya sa ta tashi a zaune ta dora hannayena a kan doron cikinta, tana shafarsa, tamkar tana rarrashinsa.Ta kuma saki dan murmushi,da ‘yar gajeruwar addu’a, don ta lura shi kansa barcin ya gagare sa, don haka ya ke janyo hankalinta da cewa ba fa ita kadai take ba. Ta kuma duban watan, cikin murmushi ta ce, ”Ba shakka, na tabbatar da ni na fi ka rashin kewa.”

Mairo ta kuma duban doron cikinta wanda a lokacin likitan da ya sallame ta daga asibiti, ya ambace shi da dan wata bakwai da sati biyu. Nan take ta ji wata irin kauna da sha’awar a ce ta haife abin da ke cikinta, ta gan sa a hannuta, ya kuma kasance ita da kanta ta yi rainon abinta da ba shi tarbiya, da duk irin kauna, da kariyar da kowace irin uwa ke yi, da tunkaho ga danta, cikin ‘yanci da walwala.

Don haka ta yi imani da ire-iren kalaman Pamela cewa babu ko tantama tana da gaskiya. Ba ta sha’awar a ce dan ta ya tashi a hannun dangin mahaifinsa,duk da kuwa zuciyar ta ta riga ta yafe ma mahaifin nasa, dangane da irin bakar ukubar da ya gallaza mata, sa’ilin yana a raye. Amma duk da haka ba ta fatar duk wani abu da zai sake hada ta da al’amarin mutanensa, don zukatansu ba annuri, ko kadan. Ko banza, ga alama zai zamo abin tozarta kamar ita, kwata kwata ba ta ra’ayin tarihi ya kuma maimaita kansa.

Ya dace da a ce, ta saki zucciyarta, ta yi tawakkali da kaddarar da ubangiji ya shimfida ga rayuwarta tare da gode masa. Zai kyautu a ce ta yi kokarin yafewa, da manta duk wani kangi da ya wakana a baya, da har take ganin tamkar duniyar ta juya mata baya, da ma duk wani da yake a cikinta. Hakan shi ya jaza kwata-kwata ba ta ra’ayin dasa wata rayuwar a gaba. Ta yi nadama matuka wanda a halin yanzu ta fi ra’ayin ‘yancin rayuwarta, a kan wannan kangin da ta tsinci kanta, na babu gaira babu dalili.
Mairo ta ga nawar Pamela ta dawo, don ta ba ta cikakken hadin kai da duk wani bayanin da za ta nema a wajenta. Ba ta fatar a ce wani, musamman ‘ya macce ta riski kanta a matsayi irin nawa, wai don kawai Allah ya halitta ta a matsayin ‘ya mace. Hakan ya sa wadansu jahillai, a cikin alumma ke kaskanta darajar ‘ya mace, sun maida ta ba a bakin komai ba. Muddin ta fice daga cikin wannan kangin, to kuwa ta daukar ma rayuwarta alwashin yada manufarta, ta yi kokarin yin amo mai karfin gaske, da ko ina cikin duniya za a ji karar sautinsa. A halin yanzu tana ganin nauyi ne da ya rataya a kanta, da muryar da ubangiji ya hore mata, don yin kokarin ceto duk wani mai rangwamen halitta daga fadawa kangi irin wanda ta tsinci kanta.

Ita kuwa Pamela yau rabonta da Mairo kusan sati daya kenan. Tun bayan sallamar da aka yi ma Mairo daga asibiti ne, ta yi balaguro zuwa Balma, amma kewarta ta addabe ta, kasancewar baya ga ita, ba wanda Mairo ke gani a matsayin nata, da ya zo ko kusa da inda take, sai fa wannan gandurobar wai ita Deborah mai kama da a kife da kwando. Kwata-kwata ba ta ko murmushi kullum cikin bakin rai take, don haka ta kan ba Mairo tausayi, (Uhm! Wai shege yi da mai zina) ko don yanayin aikin ta ne shi ya jaza mata haka, oho? Amma fa a irin nata tunanin.

Sannu a hankali sati daya ya shude,har na biyun shi ma kusan ya na dayan,shiru kake ji babu labarin Pamela. Hankalin Mairo ya yi matukar tashi, don tun da take da ita, ba ta taba wuce kwana biyu kwarara ba, ba ta zo inda take ba. Hasali ma al’amurran da suka gabata na rayuwarta, suka dinga bijirowa a cikin kwalwata, don da irin haka Bawuro ya tafi shi ma bai sake dawowa ba,… to kuma yanzu ga Pamela ita ma ta ce kwana uku za ta yi amma shiru ka ke ji. Mairo ta kai gwauro na kai mari a cikin dan dakinta na fursuna, kwatsam ta ji ana bude kyauren dakin, ga shi kuma ba lokacin cin abinci ba ne ko na fita shan iska,don ita kam ‘yar gata ce, saboda likita ya hana a sata duk wani aiki na wahala har sai ta haife abin da ke cikinta, ganin irin hadarin da ke tattare da yiwuwar faduwar cikin, gudun kada wani abu ya same ta ko dan da take dauke da shi. Mairo ta yi tsaye cak tana duban kofar da Pamela ta sunno kai ta shigo dakin,bata ankara ba, kafafuwanta suka kwashe ta inda Pamela take ta makalkaleta don murna, tamkar ta ga uwar da ta haife ta.

‘Yar karar da ta yi ta sa Mairo ta yi saurin janye jikina daga jikin Pamela ta dube ta, wanda ga alama tana cikin wani matsanancin hali. Ta kuma dubi fuskarta wadda ke da alamar kumburi a gefen idonta na hagu wurin ya yi bakikirin, abin ka da jar fata, don Pamela ruwa biyu ce mahaifiyar ta baturiya ce ‘yar asalin Faransa, mahaifinta kuwa Bafullatani ne dan asalin garin Song. Kwata-kwata sautin muryarta ya dauke, Mairo ta kasa cewa uffan. Pamela ta ja hannunta zuwa bakin gado, ta zaunar da ita kafin ta saki dan murmushi ta ce, ” Ke kuwa kamar kin ga fatalwa. Dube ki don Allah duk kin wani kanjame. Kina cin abinci da shan magungunan ki yadda ya kamata kuwa?” Ko alama ba wata alamar girgiza ko damuwa ga Pamela.Cikin al’ajabi Mairo hadiye yau da kyar ta ce, ‘’Hadari kika yi ne?’’ Pamela ta janyo ‘yar kujerar da ke dakin ta ce, ” Ba laifi, Allah ai ya kiyaye. To ya kike, ya ya bebin?”

Duk inda hankalin Mairo ya kai ya yi matukar tashi, a iya irin nacinta, ala tilas Pam ta fada gaskiyar al’amarin abinda ya sameta, na wadansu ‘yan daba da suka far mata a gida suka dake ta, tare da yi ma ta barazanar janyewa daga shari’ar da ta sa a gaba, idan kuma ta kiya to duk abinda ya same ta, to ta kuka da kanta . Pamela ba ta bar wurin da Mairo take ba,sai da ta ba ta tabbacin cewa, mai gidanta ya dauki matakai na kare lafiyarta, gami da hada ta da dogarai na musamman ba dare, ba rana, don kare lafiyarta. Pamela ta yi murna matuka ga irin sauyin da ta samu a tattare da Mairo.

**********************************************************************

Shekarar 1982, ruwan sama kamar da bakin kwarya a wani daren alhamis,shekara goma sha takwas da suka gabata, rashin kyawon hanyar da rafin garin ya yanke gadar da ta ha]a shi da sauran yankunan da ke kusa da shi, ya janyo rashin samun damar kai Fatima asibitin da ke kusa da karkararsu. Kasancewar mafi akasarin lokutta a kan keken shanu da jakkuna ake daukar marasa lafiya, idan ciwo ya yi kamari, don ba kasafai ake samun ababen hawa, irin na zamani suna shigowa yankin ba.
Ga mahaifin Mairo bai ga laifin kowa ba bisa halin da Fatima ta shiga sai rafi da gadar garin da suka ki ba su hadin kai har aka kasa kai Fatima asibitin. A wannan dare Fatima, ta kwana ta yini a durkushe tana fama da ciwon nakuda, da duk wadansu ‘yan dabaru, da ‘yan jike-jike, ba su yi tasiri a kanta ba. Shi kuwa Maigidanta, malam Dikko sai dai ya kai gauro ya kai mari a bakin ‘yar bukkar da Fatima ke a durkushe tana ta fama,sai zufa ke ta keto mata, duk da kuwa sanyin damina da ruwan sama da ake ta shekawa, a cikin daren. Daidai da assalatun fari Allah ya kaddara Fatima ta sauka. Sai dai kuma da uwar, da ‘yar da aka haifa dukkansu sun galabaita matuka, don a zaton Yafendo, kamar sauran yaran da Fatimar kan haifa can baya suna yin wabi, hakan ta kuma kasancewa a wannan karon ma. Kafin ka ce me, mahaifiyar Dikko, Nana, ta karbe ‘yar jinjirar ta dinga fesa mata ruwa tana jijjiga ta, kafin daga baya aka ji ta yankara kuka, yayin da ita Fatima jini ya yanke mata bayan an yi ta kokarin famar fitowar uwa ta biyu amma shiru kake ji. Kafin liman ya kabbara sallah, ta ce ga garinku nan.

Malam Dikko, ya yi matukar bakin cikin rashin mai dakinsa Fatima, to amma kasancewarsa Musulmi, ala tilas ya rungumi kaddara ya mika al’amarinsa ga ubangiji. Da sati ya zagayo aka rada wa jinjirar suna Maryama.Wadda mafi akasarin jama’a, suke kiranta da Mairo.

Bayan da Mairo ta isa ‘yar kimanin shekara biyar da haihuwa, mahaifinta da har a wannan lokacin bai sake kula wata ‘ya mace ba da sunan aure ba, duk da kuwa irin tsegumi da matsin lambar da mutane ake ta faman yi masa, amma ya yi kunnen uwar shegu da su. Dadin-dadawa ya saka ‘yarsa ]aya tilo da yake ji da ita kamar kwai, a makarantar boko, wanda hakan ya kara jawo ce-ce-kuce, gami da irin yadda mutanen yankin ke kyamatar ilimin boko.

Wata rana ne Mairo ta nace ma Abban nata, kamar yadda take kiran sa,da tambayar inda tata innar take, saboda ta ga duk sauran yara tsararrakinta,suna da innoninsu. Shi kuwa yakan ce mata,” Ba ga Nana nan ba, ita ma ai Innar taki ce.” Mairo ta zumburi baki ta ce masa, ” ai ita Nana ta tsufa, kuma na ji su Yafendo na cewa wai ita kawalliya ta ce.”Nana da ke bakace, ta dago kai ta dubi Mairo da Abbanta, tana ta jero masa tambayoyin inda innarta ta tafi. ”To Abba, tunda ka ce ba za ta sake dawowa ba, ka samo mani wata innar tunda Nana ta tsufa, kuma na ga innar su Abule ita ba ta tsufa ba.” Dikko ya yi kasake, ya rasa amsar da zai ba Mairo. Nana ta ja tsaki ta kwata, ta ce,” Ya ka yi shiru? ka ba ta amsa mana!”Dikko ya tada kai ya dubi Nana, ya kuma sadda kansa, yana ‘yan kame-kame.”Nana ta kuma ce masa.”Yanzu kai, saboda Allah haka ka ga zai fiye maka? Shi ke nan, ka dau abu ka kwallafa ma rayuwarka, abin da ka riga ka sani, ba ka da maganinsa ashe ba za ka yi ma rayuwar ka adalci ba, ko kana tunanin hakan da ka yi, wata dabara ce da kake ganin ka shammaci rayuwa? Kada fa ka nemi yi wa ubangiji shishigi, don gama hakan da kake yi, tamkar butulcewa ni’imarsa ce. Shi da ya ba ka ita, kuma ya karbe abin sa, ai ba fin sa son ta ka yi ba. Su kuma fa nata iyayen da suka haifa ma ka ita, su ce me?” Dikko dai ya kasa cewa uffan, ya kamo ‘yarsa ya dora ta kan }afarsa, ita kuwa ta lafe a jikinsa tamkar za ta yi kuka, ta yi lamo ganin yadda Nana ke yi masa fada. Dikko ya ka da baki ya ce Allah ya huci zuciyarku, zan gyara idan Allah ya so.

Sannu a hankali, Mairo ta sami goyon bayan su Nana da tuntuni dama suke ta fama da shi da ya sake aure har suka shawo kansa ya yarda ya sake auren da a da ya yi biris da zancen don ya dauki son duniyar nan ya dora a kan Mairo. Ko da wai ba ya kaunar ya ji kukanta, ko ya ga bacin ranta.

Mairo ba ba taba sanin abin da ke boye ba, in da ta sani da a ta matsa wa mahaifinta ya kara aure ba, domin makwafin mahaifiyarta Bulo da aka auro ita ce asasin dukkan matsalolinta da abin da ya faru da ita daga baya. Baya ga wadannan matsaloli, ga maraici, sa’annan aka yi mata aure tun tana karama. A cikin wannnan babban gida Mairo ta ci gaba da rayuwa a tsakanin mata uku da suka shiga gasa mata gyada a tafin hannu. Daga wannan sharri yau zuwa wancan kulli daga karshe aka zarge ta da kashe mijinta, aka shiga kotu, nan ma ta rasa madafa; ga ciki, ga kuma tsoron abin da karshen shari’a zai kasance, Mairo ta rasa abin da ke mata dadi a rayuwa. Tunaninta daya shi ne ko Pamela za ta iya fitar da ita daga wannan daurin gwarmai…

TAKAITACEN TARIHIN MARUBUCIYAR
An haifi Halima Ahmad Matazu a garin Zaria na jihar Kaduna, a ranar 10 ga watan Nuwamba shekarar 1978 Miladiya. Halima Ahmad Matazu ta fara karatu a Makarantar Elebester ta ara kanana, sannan ta yi karatun Firamare a Kwlejin Gwamnatin Tarayya da ke Sokoto, ta yi karamar Sakandire a makarantar ‘Yan mata ta Nana, da ke a garin Sakkwato. Daga bisani ta karasa karatun babbar Sakandire a Kwalejin Kimiya ta ‘Yan mata da ke garin Sandamu, yankin Daura ta jihar Katsina, a shekarar 1996. Daga nan ta shiga fagen neman digiri a Jami’ar Usman Dnfodiyo da ke Sakkwato a shekarar 1997, inda ta kammla da samun digiri a fannin harshen Hausa a shekarar 2002. Bayan nan ta yi bautar kasa a jihar Katsina a Kwalejin Gwamnati ta jiha (G.C.K). Littafin Amon ‘Yanci shi ne littafinta na farko da ta wallafa. Halima Ahmad Matazu, ta yi aure, tana zaune a garin Katsina.

scroll to top