Close

Ban Taba… na Maryam Aliko Mohammed

Ban taba…. Ban taba tsammanin zai ci amana na ba haka.

Ni, yar gaban goshin sa, mai ilimin cikin su, ni wacce na fi kowa fahimtar halin sa.

“Ita likita ce” ya ce. Amma na tabbata sakamakon takaddun ta na karatun likita, daga Jami’ar Jos,na bogi ne. Ya ce “yanzu ta kara fahimtar sa sosai da girma ya zo; da ya tsufa ba? Sannan za ta iya taimaka ma na da ciwon sugan sa ba, mceww!

Tabdi jam!

Ya fada min cewa kada na damu, kuma ya tabbatar min cewa ba wani abin kirki za ta amfana da shi ba; ba zai iya biya mata bukatar ta ba.” Ciwon sugan nan ne ai. Ta zo ne don ta taimaka da ciwon sugan” ya tabbatar min.

Kin ji mamakin da na ji sanda mu ke fada, na ja hijabin ta, lokacin ne na ji girman kunburin cikin ta kaman mai tsohon ciki.

Ban taba….

I Never…
I never thought that he would betray me this way.

I, his favourite, the educated one, the one that understood him the most.

She is a medical doctor, he says. But I am sure her certificate is fake from ABU Jos. He says she understands him more now that he is grown; grown old ba? And she is able to help with his diabetes, mchew!

Imagine!

He has told me not to worry, and assured me she will not get much from the deal; he is unable to exercise his conjugal rights. “It’s the diabetes you see. She is only here to help with the diabetes,” he assured me.

Imagine my shock when we were fighting and I grabbed her hijab, that was when I felt her rounded and very pregnant belly.

I never…

  • TAGS
  • Ban Taba
  • Hausa Story
  • Maryam Aliko Mohammed
scroll to top